Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA: Figo ya nemi a yi muharawa

Tsohon zakaran kwallon duniya Luis Figo ya bukaci a gudanar da muharawa tsakanin shi da ‘yan takara hudu da ke neman kujerar shugabancin hukumar FIFA. Ga alamu Figo ya zama babban mai adawa da shugaba Sepp Blatter mai neman wa’adi na biyar a FIFA .

Luis Figo
Luis Figo Reuters
Talla

Tuni Yariman Jordan Ali bin Al Hussein ya kawo shawarar yin muharar bayan ya bayyana aniyar kalubalantar Blatter a zaben FIFA da za’a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.

Figo wanda tsohon dan wasan Real Madrid ne da Barcelona ya yi alkawalin dawo da martabar FIFA musamman game da badakalar rashawa da ta dabaibaiye hukumar yanzu haka.

Daga cikin manufofin shi, Figo ya ce zai kara yawan kasashen da ke fafatawa a gasar cin kofin duniya zuwa 48 sabanin 32.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.