Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta fara Hukunta wanda ke aikata laifin nuna kabilanci

Firiya Minista Kasar Fransa Manuel Valls ya dau alkawalin hukunta duk wanda aka kama, da aikata laifin nuna kabilanci ko kinjinin yahudawa a kasar.Matakin na zuwa ne a yau juma’a bayan kasar ta kaddamar da Shirin yaki da kabilancin tare da kin jinin yahudawa

Firaministan Faransa,Manuel Valls
Firaministan Faransa,Manuel Valls REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Daga yanzu duk wani laifin nuna kabilanci ko kyamar yahudawa da musulmi a kasar ta Faransa, ba zai wuce haka kaiwa ba tare da zartar da hukumci mai tsanani a kansa

Idan dai ba a manta ba a ranar 31 ga watan december bara, a lokacin da yake taya faransawa murnan zagayowar sabuwar shekara ta 2015, shugaban kasar Faransa François Hollande ya bayyana yaki da kabilanci da kuma kin jinin yahudawa a matsayin babban al’amari da gwamnatinsa ta sa gaba

yanzu kuma Firiya Minista kasar ta Faransa Manuel ne a yau juma’a ya yi filla filla da yadda yakin zai kasance a karkashin manufofinsa

Nuna kabilanci da kin jinin yahudawa da musulunci na ci gaba da fadada a kasar Faransa abinda Valls yace nauyin da ya rataya a wuyansu su san yadda yadda zasu a kawo karshen annobar

har ila yau Mr Valls ya ce Faransawan Yahudawa, bai dace su ci gaba da kasancewa cikin fargabar kasancewarsu yahudawa ba a Faransa, haka suma musulmin Faransa babu wata hujjar da ci gaba da jin kunya ko boye matsayinsu na musulmi a kasar ba

Daga cikin jerin matakan yaki da nuna wariya, ko kabilanci a Faransa, akwai Euro miliyan 100 da gwamnatin ta kebewa domin yin yakin dasu a cikin shekaru uku nan gaba, a yayin da hukuncin kotu zai zama mai tsauri a kan laifin nuna kabilanci ko kin jinin yahudawa, wanda ya zama wata sabuwar doka a cikin kundin shara’ar kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.