Isa ga babban shafi
Faransa

Har yanzu Fadar Fafaroma ba ta amince da jakadan Faransa ba

Watanni uku bayan da kasar Faransa ta nada wani fitaccen dan luwadi a matsayin jakadanta a fadar Fafaroma na Vatican, har yanzu Faransa na dakon amincewar fadar Fafaroman

Shugaban Faransa Francois Hollande da Fafaroma Francis
Shugaban Faransa Francois Hollande da Fafaroma Francis AFP PHOTO POOL / GABRIEL BOUYS
Talla

Wannan al-amari dake zuwa a daidai wani lokaci da Fafarona Francis ke shirin shiga shekaru uku da fara aiki, yasa masu lura da lamurran yau da kullum na ganin cewa shirun da fadar Fafaroma tayi na nuna kila an sami sauyin ra’ayi.

A baya dai fadar Fafaroma kan furta amincewarta da nadin jakada da aka gabatar mata cikin wata daya ne.

Ita dai Faransa ta nuna cewa shi jakada Laurent Stefanni mai shekaru 55 ta ke bukata a fadar Fafaroman.

Wasu majiyoyi na cewa shine zabin shugaban Faransa Francois Hollande da ministocin kasar.

Wata majiya ta nuna cewa fadar Paparoman basa raayin masu luwadi yanzu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.