Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na bitar dokar leken sirrin jama'ar Kasar

Majalisar dokokin kasar Fransa na ci gaba da yin bitar farko kan wata ayar doka da ta bukaci baiwa gwamnati karfin iko wajen gudanar da binciken da ya hada da leken asiri ga al’ummar kasar, yayin da kungiyoyin kare hakkin adam ke ci gaba da sukar dokar

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande REUTERS/Eric Feferberg/Pool
Talla

Duk da cewa harin ta’addancin watan janairun da aka kai a birnin paris ne, yayi sanadiyar bijiro da bukatar kafa dokar, bata tsaya kan yaki da ayyukan ta’addanci ba a kasar.

Sai dai za a iya cewa, dokar ta samar da hurumi ga ayyukan samar da bayanan siri ne ga gwamnati, da har yanzu a karkashin dokokin kasar ba a kayyade mata iyaka ba , wanda hakan ya kasance nakasun da zai iya haifar da fushin kungiyar tarayyar turai, kuma ya sa ta dauki matakan ladabtarwa a kan kasar ta Fransa.

Ita dai wannan doka da gwamnatin Fransa ta gabatar wa majalisar dokokin ta kunshi matakai guda 7 ne, dake baiwa jami’an leken asirin kasar cikakken iko a cikin aikin gudanar da bincike.

Daga kare hakkin kasa, yaki da ayyukan ta’addanci zuwa yaki da masu aikata laifuka, dake kunshe a dokar, yasa masana dokoki a faransa na kallon dokar a matsayin mai fadi sosai, da yasa suke fargabar zata iya shafar yancin da al’ummar da suke dashi a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.