Isa ga babban shafi
Ukraine

Faransa da Jamus za su jagoranci tattaunawar sulhu akan Ukraine

Shugabannin Kasashen Faransa da Jamus da Ukraine za su gudanar da wani taro tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a ranar laraba mai zuwa a kokarin da suke na kawo karshen zub da jinin da ake yi a kasar Ukraine.

Angela Merkel ta Jamus, Petro Poronshenko na Ukraine da Shugaban Faransa Hollande
Angela Merkel ta Jamus, Petro Poronshenko na Ukraine da Shugaban Faransa Hollande Crédits photo : SERGEI SUPINSKY/AFP
Talla

Matakin na zuwa ne bayan shugabanin kasashen hudu sun tattauna a tsakaninsu ta waya don ganin an samu tsagaita wuta tsakanin ‘yan tawayen da ke samun goyan bayan Rasha da kuma sojojin gwamnatin Ukraine.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, da shugaba Francois Hollande na Faransa sun kaddamar da wani yunkurin diflomasiya tsakanin gwamnatocin Kiev da Moscow inda suka gana da bangarorin biyu don ganin an magance tashin hankalin da ake samu.

Sai dai shugaba Vladimir Putin ya ce samun nasarar taron ya danganci amincewa da wasu sharudda da suke ci gaba da mahawara akai a ganawar da suka yi da shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko.

Yau ake saran ministocin kasashen za su gudanar da wani taron share fage kafin taron shugabanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.