Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine-Amurka

Kokarin samar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine

Kasashen Yammacin duniya na ci gaba da yi wa shugaban Rasha Vladimir Putin matsin lamba domin ya amince da shirin da shugaban Francois Hollonde na Fransa da kuma Angela Merkel ta Jamus suka gabatar masa domin warware rikicin kasar Ukraine.

Talla

A taron samar da zaman lafiya da aka gudanar a birnin Munich na kasar Jamus a jiya asabar, shugabannin sun bayyana cewa akwai bukatar shugaban Putin ya fito fili ya nuna wa duniya cewa yana fatar samar da mafita ga rikicin na Ukraine wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu biyar kawo yanzu.

A cikin makon da ya gabata ne shugaba Hollande da kuma Merkel suka gaba da shugaban Ukraine da na kuma Rasha domin gabatar masu da wani shirin zaman lafiya, to sai dai kasashen na Yamma na da shakku a game da ko Ra Moscow za ta aiwatar da shirin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.