Isa ga babban shafi
Najeriya

An sallami jirgin Rasha da aka kama a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sallami jirgin Rasha da ta kama dauke da makamai a birnin Kano bayan Jami’an tsaron kasar sun kammala bincikensu tare da gamsuwa da ikirarin Rasha da Faransa na mallakar kayan da ke cikin jirgin.

Jirgin Rasha da aka kama a garin Kano Najeriya
Jirgin Rasha da aka kama a garin Kano Najeriya RFI/Dandago
Talla

Kakakin sojin saman kasar Air Marshal Olusola Amosun ya bayyana haka a jawabin da ya yi wa manema labarai tare da jami’in tsaron ofishin Jakadancin Faransa Kanal Marcc Humbert.

Amosun yace an tsare jirgin ne saboda rashin cikakkunn bayanai amma yanzu sun gamsu da bayanin da ofishin jakadancin Faransa ya yi musu saboda haka an saki jirgin mai dauke da matuka 18 ‘yan Rasha da 2 daga Faransa.

Tuni dai Jekadan Faransa Jacques Champagne de Labriolle ya tabbatar da cewa kayan da ke cikin Jirgin mallakinta Faransa ne.

A cewarsa Faransa za ta bi da kayan ne ta Chadi zuwa ga dakarunta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

An dai bayyana cewa Jirgin ya sauka Kano ne saboda matsalolin da suka shafi rashin samun damar sauka a Chadi.

Wasu ‘Yan Najeriya dai na zargin kayan da ke cikin jirgin ire-irensu ne ake amfani da su wajen kai hare hare a cikin kasar.

A ranar Assabar ne mahukuntan Najeriya suka kama jirgin dauke da kayan yaki a garin Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.