Isa ga babban shafi

Najeriya ta fara biyan diyyar naira biliyan 2 kan aikin hanyar Lagos zuwa Calabar

Ma’aikatar Ayyuka a Najeriya ta sanar da fara biyan diyyar kudin da yawansa ya kai naira biliyan 2 da miliyan 750 ga mutanen da aikin ginin babbar hanyar Lagos zuwa Calabar zai shafi filaye da gidajensu.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kenan.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kenan. © premiumtimes
Talla

 

Ministan Ayyuka na Najeriyar David Umahi da ke sanar da wannan mataki yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a jihar Lagos ta Kudu Maso Yammacin kasar ya ce, tun a jiya Laraba gwamnatin kasar ta fara aikin biyan kudaden wanda ke matsayin wani bangare na diyyar da za ta biya yayin wannan aikin titi ga mutanen da aikin shimfida babbar hanyar ta Lagos zuwa Calabar zai shafi kadarorinsu.

A cewar Ministan Ayyukan na Najeriya Mr Umahi biyan diyyar tausayawa ce da kuma kyautatawa ga al’ummomin yankin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen zaben shugaba Bola Tinubu a zaben da ya gabata.

Aikin hanyar mai tazarar kilomita 700 da aka yi ittifakin kowacce kilomita guda za ta lashe kudin da yawansa ya kai naira biliyan 4 gabanin kammaluwarsa, tuni ya haddasa cece-kuce a sassan kasar mafi yawan jama’a a Afrika.

Bayanai sun ce tun a yammacin jiya Mr Umahi ya damka takardun cek na kudi da mutanen da za su karbi diyyar kadarorin nasu, bayan da ya bayyana hanyar a matsayin mai muhimmancin da za ta janyo hankalin masu yawan bude ido a cikin kasar mafi karfin tattalin arziki a nahiyar.

Wasu bayanai na cewa adadin kudaden fansar na naira biliyan 2 da miliyan 750 na matsayin kudaden fansar kashi 3 na rukunnin farko na ginin titin da gwamnatin Najeriyar za ta biya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.