Isa ga babban shafi
Kamaru-Najeriya

Kamaru ta kama Mayakan Boko Haram da dama

Majiyoyin tsaron soja da na ‘yan sanda a kasar Kamaru sun ce sun yi nasarar kama ‘ya‘yan kungiyar Boko Haram a garin Edea da ke cikin Jahar Sanaga mai tashar jiragen ruwa a yankin arewacin kasar. Kuma majiyoyin sun ce a ranar Assabar shida ga watan Disemba ne aka cafke Mayakan na Boko Haram.

Sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram à Dabanga
Sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram à Dabanga AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Majiyar ta kara da cewa, ‘yan Boko Haram da dama ne a aka kama a garin na Edea da ke yankin nan mai makwabtaka da birnin Yawunde.

Bayanai sun ce ‘yan kungiyar ta Boko Haram na yinkurin kutsa kai ne zuwa birnin Yawunde babban birnin kasar taKamaru a lokacin da jami’an tsaron suka kamasu a wajen binciken shingen tsaro da ke arewacin garin na Edea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.