Isa ga babban shafi
Turai

WHO tace murar tsuntsaye zata ci gaba da yaduwa a Turai

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace cutar murar tsuntsayen da aka samu a nahiyar Turai zata ci gaba da yaduwa a Yankin, inda hukumar ta WHO ta bukaci sa ido a kai.Jami’ar hukumar lafiyar dake kula da murar tsintsaye Elizabeth Mumford, tace ganin yadda cutar ke yaduwa suna da fargaba kar ta kama Bil Adama, saboda haka suna bukatar mutane su sa ido akai.Mumford ta bayyana muhimmancin kashe tsintsayen da suka kamu da cutar ko kuma suka fara nuna alamun rashin lafiya, da kuma sa ido kan mutanen dake fama da rashin lafiyar.Ya zuwa yanzu dai an gano cutar da ake kira H5N1 a kasashen Holland da Jamus, wadda tayi kama da wanda aka samu a kasashen China, Japan da Koriya ta Kudu.An kuma samu labarin makamancin haka a Britaniya, ko da yake ana ci gaba da gudanar da bincike a kai.Wani fitaccen masanin cutar, mai suna Ron Fouchier yace hukumomin Britaniya sun bayyana cewar cutar da aka gano a kasar su irin ta kasar Jamus ne. 

Kwararru suna aiki a kan kajin da ake zargi suna dauke da cutar H5N1
Kwararru suna aiki a kan kajin da ake zargi suna dauke da cutar H5N1 REUTERS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.