Isa ga babban shafi
FARANSA

Mutane 2 sun mutu sanadiyar cutar Murar Aladu a Faransa

Hukumar kiyon lafiya a kasar Faransa ta bada sanarwar barkewar cutar Murar Aladu ta A(H1H1) inda mutane 176,000 suka kamu da cutar biyu kuma daga cikinsu suka mutu. Likitoci a hukumar kiyon lafiyar sun bayyana cewa mutane 174 cikin dari ne ke kamuwa da cutar a kowane mako. An dai bayyana nau’oin cutar murar aladu guda uku da ke addabar al’ummar kasar, tun bayan fara barkewar cutar a shekarar 2009.A Birtaniya ma hukumomin kiyon lafiya a kasar sun ruwaito mutuwar mutane 27 sanadiyar kamuwa da cutar.A yanzu haka dai hukumomin kiyon lafiya a kasashen biyu suna karfafawa al’umma gudanar da rigakafi musamman masu manyan shekaru da cutar tafi kamawa.A wani bincike da hukumar kiyon lafiya ta duniya WHO ta gudanar, binciken ya nuna cewa duk shekara mutane akalla miliyan biyar ne ke kamuwa da cutar a kasashen duniya kuma a cikinsu mutane 250,000 zuwa 500,000 ke mutuwa duk shekara. 

Dakin binciken rigakafin cutar Murar Aladu ta H1N1
Dakin binciken rigakafin cutar Murar Aladu ta H1N1 Felix Ordonez/Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.