Isa ga babban shafi
FARANSA

Faransa ta yi kira ga Faransawa su kaura daga Cote d’Ivoire

Gwamnatin kasar Faransa ta yi kira ga daukacin faransawa mazauna kasar Cote d’ivoire kimanin 15,000 da su kaura daga kasar don gudun barkewar yakin basasa a kasar, kamar yadda mai Magana da yawun gwamnatin kasar Francois Baroin ya sanar a yau laraba.Wannan dai na zuwa ne lokacin da majalisar zartarwar kasar ke ganawa a yau laraba, inda gwamnatin kasar ta bayyana gargadin a amtsayin rigakafi ga al’ummar kasar dake zaune a Cote d’Ivoire.Kasar Cote d’Ivoire wacce a yanzu ke cikin mawuyacin halin rikicin siyasa tun bayan kammala zabe wanda shugaban kasar Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara dukkaninsu ke ikirarin lashe zaben kujerar shugabancin kasar 

Minstan kasafin kudin faransa François Baroin da Francois Fillon, prime Minster Faransa
Minstan kasafin kudin faransa François Baroin da Francois Fillon, prime Minster Faransa REUTERS/
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.