Isa ga babban shafi
Scotland

Al'ummar Britaniya suna kira ga 'yan Scotland kar su kada kuri'ar ballewa

Firaminsitan Britaniya David Cameron na kan hanyar shi ta komawa Scotland, dan ci gaba da rarrashin al’ummar kasar da su kaucewa kada kuri’ar amincewa da samun yancin kan yankin daga Britaniya, a zaben da za’a gudanar ranar Alhamis mai zuwa.Rahotanni sun ce yanzu haka masu neman yancin da masu adawa, na tafiya kafad da kafada a kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar.Ko a jiya Lahadi, Sarauniyar England Elizabeth ta Biyu, ta yi kira ga al’ummar Scotland da suyi dogon nazari kafin kada kuri’ar tasu. 

Fraiministan Britaniya, David Cameron
Fraiministan Britaniya, David Cameron REUTERS/Luke MacGregor
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.