Isa ga babban shafi
Britaniya

Britaniya ta nemi kungiyar EU ta aika da masu sa ido zuwa iyakar Jibrolta

Firaministan kasar Birtaniya, David Cameron ya yi kira ga kungiyar Tarayyar Turai da ta aika da masu sa ido kan iyakar Jibrolta, domin su ganewa idonsu yadda Spain ke gudanar da bincike akan iyakar, lamarin da ya haifar da cunkosun masu ababan hawa.A ‘yan kwanakin nan ne dai takaddama ta barke tsakanin kasashen biyu, bayan kasar Spain ta gina wani shingen bincike, wanda hakan bai yiwa Birtaniya dadi ba.Kungiyar tarayyar ta Turai dai ta ce, za ta aika da masu saka idon, nan da watan Satumba ko kuma Oktoba, sai dai Firaministan Birtaniya ya ce ya yi jinkiri da yawa. 

Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron
Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron REUTERS/Matt Cardy/POOL
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.