Isa ga babban shafi
Scotland

Idon duniya yana kan Scotland-Salmond

Babban mai da’awar fafutikar tabbatar da ‘Yancin kai a kasar Scotland, Alex Salmond ya bayyana fatar samun nasara a zaben raba gardama da za’a gudanar a makon gobe domin cim ma bukatunsu na ballewa daga Ingila tsawon shekaru 307.

Alex Salmond na Scotland
Alex Salmond na Scotland REUTERS/Russell Cheyne
Talla

Mr Salmond yace Scotland na kan anyar kafa tarihi domin idon duniya yana kan kasar. a cewarsa mutanen Scotland zasu kada kuri’ar amincewa a ranar Alhamis mai zuwa kuma amincewa da wannan alkawali ba zai zama yaudara ga kowa ba.

Salmond yace sako ga mutanen Scotland shi ne a tarihi a ranar 18 ga Satumba, za su tantance makomar kasarsu da kansu.

Kafofofin yada labaran Birtaniya sun ruwaito cewa kimanin kashi 97 na mutanen kasar ne suka yi rijistar kada kuri’a, cikinsu hard a ‘yan kimanin shekaru 16 zuwa 17 da aka amince su jefa kuri’a.

Amincewa da ‘Yancin Scotland zai kawo karshen shekaru 307 na zama tsakanin Ingila da Scotland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.