Bincike ya nuna cewa akwai 'ya 'yan baki da dama a makarantun Britaniya
Sabbin Alkalumman gwamnatin da aka fitar a bangaren Ilimi a kasar Burtaniya sun nuna cewar akalla Dalibai Miliyan 1 masu karatu a Makarantun gwamnatin kasar basa magana da Harshen Turanci a matsayin harshen Uwa.Wannan dai ya nuna cewar akalla Dalibi 1 cikin 6 na Dalibai da gwamnatin kasar Burtaniya ke daukar dawainiyarsu ba Turanci ne harshensu na Uwaba.A taikaice dai kashi 16.6 na Daliban ba ‘yan haifen kasar Burtaniya mai daukar dawainiyar karatunsu ba ne.Mai magana da yawun bangaren ilimi a kasar yace, a lokacin da daliban suka kai shekaru 16, yayin rubuta jarabawar kammala Sakandare, yaran da ke amfani da turanci a matsayin harshe na biyu, suna cimma wadanda suke iyayensu Turawa ne.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: