Ukraine: Rasha za ta fuskanci sabbin takunkumi
Shugaban Faransa Francois Hollande yace Kungiyar Tarayyar turai zata tsaurara wa kasar Rasha takunkumi a taron da shugabannin kungiyar zasu gudanar a birnin Brussels akan rikicin kasar Ukraine.
Wallafawa ranar:
Hollande yace ko shakka babu hukumar Tarayyar Turai zata karfafa wa kasar Rasha takunkumi saboda ruwa da tsaki da Rasha ke yi a rikicin kasar Ukraine.
Tuni dai kungiyar tsaro ta NATO tace Sojojin Rasha sun shiga Ukraine domin taimakawa ‘Yan tawaye da ke fada da gwamnatin kasar.
Idan an jima ne dai shugabannin kasashen Turai zasu gudanar da taro a Brussels domin tattauna batun rikicin Ukraine, inda shugaban kasar Petro Poroshenko, ke fatar kungiyar Turai zata dauki tsauraran matakai akan Rasha da ke goyon bayan ‘Yan a ware da suka mamaye gabacin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu