Isa ga babban shafi
Ukraine

Poroshenko ya shata hanyar samun zaman lafiya a Ukraine

Shugaba Kasar Ukraine Petro Poroshenko ya yi alkawarin shata hanyar kawo karshen tashin hankalin da ake tsakanin sojojin kasar da ‘Yan Tawayen da ke samun goyan bayan Rasha. Bayan ganawar da Poroshenko ya yi da Vladimir Putin, shugaban na Ukraine ya yi alkawarin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar ta za ta kai ga kawo karshen tashin hankalin da ya yi sanadiyar rasa dimbin rayuka.

Shugaban Kasar Ukraine, Petro Poroshenko
Shugaban Kasar Ukraine, Petro Poroshenko REUTERS/Olivier Hoslet
Talla

Shugaban yace nan da dan lokaci kadan za’a rubuta yarjejeniyar wadda zata kunshi tsagaita wuta daga kowanne bangare, yayin da Shugaba Putin ya yi alkawarin taimakawa wajen sasantawa, sai dai yace samun duk wata nasara na hannun gwamnatin Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.