Isa ga babban shafi
Ukraine

‘Yan tawayen Ukraine sun harbo Jirgin kasar

Rundunar Sojin kasar Ukraine tace ‘Yan Tawayen da ke samun goyan bayan Rasha sun harbor jirgin yakin kasar a Yankin da ke ci gaba da ruwan wuta tsakanin bangarorin biyu. Kakakin sojin, Andriy Lysenko yace an harbor jirgin kirar SU-25 a sararain samaniya, kuma yanzu haka ba a san halin da matukinsa ke ciki ba.

Mayakan a ware na Ukraine a Makiïva
Mayakan a ware na Ukraine a Makiïva REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Hukumar Kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane 415, 800 suka tserewa gidajen su a Ukraine sakamakon fafatawar da ake tsakanin Yan Tawaye da sojin gwamnati.

Kididigar hukumar ya nuna cewar 190,000 sun warwatsu a cikin kasar, 197,400 sun tsallaka kasar Rasha, 14,600 sun shiga kasar Poland yayin da 13,883 suka tsallaka zuwa kasar Belarus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.