Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

‘Yan tawaye sun harbo Jirgin Ukraine

‘Yan tawaye da ke gwagwarmayar warewa daga Ukraine sun harbo wani karamin jirgin yakin kasar kafin soma tattaunawar gaggawa da Faransa da Jamus zasu jagoranta tsakanin wakilan Ukraine da Rasha a birnin Berlin.

Jami'an tsaron kare iyaka na Ukraine a  Donetsk
Jami'an tsaron kare iyaka na Ukraine a Donetsk REUTERS/Valentyn Ogirenko
Talla

Za’a yi tattaunawar ne tsakanin Ministocin harakokin wajen Rasha da Ukraine da Jamus da Faransa a Berlin.

Rundunar Sojin Ukraine ta shaidawa Kamfanin Dillacin labaran Faransa cewa a harbo jirgin yakinta MiG-29 daga sararin samaniya a kan hanyarsa ta kai wa ‘Yan tawayen farmaki a yankin Lugansk.

Rundunar Sojin tace matukin jirgin ya yi amfani da lemar jirgi domin tsira da ransa.

Kafin soma tattaunawar kuma, gwamnatin Ukraine ta zargi Rasha da cilla makaman Roka a yankin kasarta.

Mahukuntan Ukraine sun ce wasu ayarin motocin Soji dauke da makamai sun tsallaka kan iyakar kasar zuwa wani kauye da ke cikin lardin Lugansk da ‘Yan tawaye ke iko.

Wannan zarge zargen kuma baraka ce ga zaman sulhu tsakanin bangarorin biyu a Berlin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.