Rasha
Rasha ta haramta shigo da kayan abinci daga Turai da Amurka
Kasar Rasha ta haramta shigo da wasu na’uin kayan abinci daga kasashen Turai da Amurka a wani mataki da ake ganin martani ne ta fara mayarwa akan akan takunkumin kariyar tattalin arziki da suka kakaba ma ta saboda rikicin Ukraine. Rasha kuma ta yi barazanar haramtawa jiragen Turai da Amurka yin amfani da sararin samaniyarta. Amma Kungiyar Turai ta yi watsi da matakin na Rasha tare da cewa zata dauki mataki akai.
Wallafawa ranar:
Talla
Nau’in kayan abincin da Rasha ta haramta shigowa da su sun kunshi kayan marmari da Kifin gwangwani da Nama da Madara da sauransu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu