Isa ga babban shafi
Ukraine

Ukraine tace dakarun Rasha sun karbe Novoazovsk

Gwamnatin kasar Ukraine tace Dakarun kasar Rasha sun karbe ikon garin Novoazovsk da ke kan iyaka da kasashen biyu a kudu maso gabacin Ukraine inda ake gwabza fada tsakanin ‘Yan tawaye da dakarun gwamnatin kasar. Babbar Majalisar tsaron kasa ta Ukraine a cikin wata sanarwa a Twitter tace Rasha ta kuma karbe ikon kauyukan da ke yankin .

"yan tawayen Ukraine a yankin Novoazovsk
"yan tawayen Ukraine a yankin Novoazovsk AFP PHOTO / ALEXANDER KHUDOTEPLY
Talla

Yanzu haka shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya katse ziyarar day a shirya kai wa zuwa Turkiya a yau Alhamis domin jagorantar taron gaggawa na tsaro domin daukar mataki akan Rasha.

Amurka tace hakan ya tabbatar da cewa kasar Rasha tana da hannu dumu dumu a rikicin kasar Ukraine, wajen taimakawa ‘Yan a ware da ke kishin ta.

Bayan kwashe makwanni sojojin gwamnatin na samun nasara, yanzu haka ‘Yan Tawayen sun yunkuro abin da yasa gwamnati ta bukaci taimakon kungiyar kawacen tsaro ta NATO domin kai musu dauki.

Wakilin kanfanin dillancin labaran Faransa yace babu koda sojan gwamnati guda a kudancin Donetsk yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.