Isa ga babban shafi
Ukraine

Mutane 2,600 aka kashe a rikicin Ukraine

Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane 2,600 aka kashe a rikicin da ake yi a gabacin Ukraine tsakanin ‘Yan a ware da gwamnatin kasar. Rahoton yace adadin mutane 2,593 aka kashe tsakanin Watan Afrilu zuwa Agusta na wannan shekarar ta 2014.

'Yankin Donetsk a gabacin Ukraine da 'Ya tawaye suka mamaye
'Yankin Donetsk a gabacin Ukraine da 'Ya tawaye suka mamaye REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da ma’aikatar tsaron kasar Rasha ke karyata zargin da Amurka da Ukraine ke yi wa Sojojinta, na shiga rikicin da ke ci gaba da zafafa tsakanin dakarun Ukraine da ‘yan a waren kasar.

Mai Magana da yawun ma’aikatar Igor Konashenkov, yace dakarun kasar da ake rade radin sun haurawa zuwa Ukraine ba wani abu suke yi ba sai atisaye na kashin kansu.

Wannan ne karon farko da wani babban jami’n gwamnatin kasar ya mayar da martani kan zargin da Amurka ke wa hukumomin birnin Moscow na bai wa ‘yan tawayen tsaro ta sama, da ma shi ga cikin rikicin na Ukraine.

Hukumomin kasar Ukraine, da wasu kasashen yammacin duniya sun ce Rasha na da hannu, dumu dumu a rikicin da ‘Yan tawayen kasar ke naman kafa kasa mai cin gashin kanta.

Shugaban Amurka, da ya jagoranci sauran kasashen duniya da ke Allah wadai da yakin na gabasghin Ukraine yace sojojin Rasha ne ke yakin, duk da hukumomin birnin Moscow sun karyata hakan.

Mr Obama da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun yi gargadin cewa matakan da Rasha ke dauka zasu koma kanta, lamarin da ake ganin gargadi ne kan yiwuwar Karin takunkumi.

Kungiyar tsaro ta NATO tace akwai a kalla sojan Rasha 1,000 da ke tallafawa ‘ya a ware, da ke yaki da hukumomin birnin Kiev tun cikin watan Afrilu.

Jekadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power, da ke magana a zauren taron kwamitin tsaro na Majalisar ta nemi Rasha ta dai na boye gaskiya, tana mai cewa yanzu gaskiya ce ta bayyana.

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko, yace kasar na cikin mawuyacin hali, sai dai a cewar shi, ba zasu firgita ba, don akwai mafita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.