Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya bukaci a yi wa gwamnati garambawul

Yanzu haka dai Firaministan kasar ta Faransa Manuel Valls ya soma tattaunawa da mukarrabansa kan yadda zai kafa sabuwar gwamnati kamar dai yadda shugaban kasa Francois Hollande ya bukace shi ya yi.

Manuel Valls da Arnaud Montebourg
Manuel Valls da Arnaud Montebourg AFP/Philippe Desmazes
Talla

To sai dai tuni aka tabbatar da cewa ministan kudin kasar Arnaud Montebourg ba zai ci gaba da rike mukaminsa a sabuwar gwamnatin da za a kafa ba.

Fransa dai na fama da matsalar tattalin arziki lamarin da ya yi sanadiyyar korar tube tsohon Firaminista da kuma danka ragamar a hannun Manuel Valls yau kusa da watanni 4 da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.