Valls ya kafa sabuwar gwamnati a Faransa
Sabon Firaministan kasar Faransa Manuel Valls ya sanar da kafa majalisar ministoci, kwana daya bayan da ya karbi ragamar tafiyar da wannan mukami daga hannun wanda ya gabace shi Jean-Marc Ayrault.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wasu daga cikin sabbin fuskoki a wannan gwamnati har da Segolene Royal wadda aka bai wa mukamin ministan kare muhalli, yayin da ministan tsaro da na harkokin waje a gwmanatin da ta gabata, Jean-Yves le Drian da kuma Laurent Fabius za su ci gaba da rike mukamansu.
A ranar talata ta makon gobe ce Manuel Valls zai je gaban Majalisar Dokokin kasar domin salon siyararsa a gaban majalisar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu