Isa ga babban shafi
Faransa

Sabon Firaminista Valls ya karbi ragamar mulki daga Ayrault

Sabon Firaministan Faransa Manuel Valls yana shirin kafa sabuwar gwamnati da zummar farfado da darajar gwamnatin gurguzu ta shugaba Francios Hollande da ba su sha da dadi ba a zaben kananan hukumomi da aka kammala a karshen mako.

Jean-Marc Ayrault kafin mika ragamar mulki a hannun Manuel Valls
Jean-Marc Ayrault kafin mika ragamar mulki a hannun Manuel Valls AFP PHOTO / PATRICK KOVARIK
Talla

Manuel Valls ministan cikin gida ne kafin ya karbi mukamin Firaminista a gwamnatin Gurguzu ta Francios Hollande da ke mulki a Faransa.

babban kalubalen da ke gaban Mista Valls mai shekaru 51, shi ne kokarin farfado da tattalin arzikin Faransa. Tare da magance matsalar rashin aikin yi da ya dushe farin jinin gwamnatin gurguzu ta Francios Hollande da ta yi yanzu shekaru biyu saman mulki.

Wannan kalubalen ne dai ya sa Jam’iyyar gurguzu ba ta sha da dadi ba a zaben kanana hukumomi inda shugabancin manyan biranen Faransa ya fado a hannun ‘Yan adawa da kuma Jam’iiyar ‘Yan kishin kasa.

Wani batu kuma da ke gaban mista Valls shi ne kokarin dinke barakar cikin gida ta Jam’iiyar Gurguzu, inda wasu daga cikin ministocin Jam’iyyun Hadaka suka ce zasu fice sabuwar gwamnatin Valls.

Masu fashin bakin siyasar Faransa suna ganin sai mista Vallas ya samu hadin kan Jam’iyyarsa kafin ya iya fuskantar kalubalen da ke gabansa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.