Isa ga babban shafi
Faransa

Bukukuwan ranar 'yancin a Faransa

A wannan litinin 14 ga watan Yuli, ita ce ranar ‘yanci a Faransa, inda shugaban kasar Francois Hollande ya duba wani faretin soja na hadi-gwiwa a gaban aki daga kasashen duniya akalla 76 wadanda suka taka rawa domin taimaka wa kasar a yakin duniya na daya.

Sojojin Faransa na fareti ranar 14 ga watan Yulin 2014 a Paris
Sojojin Faransa na fareti ranar 14 ga watan Yulin 2014 a Paris REUTERS/Charles Platiau
Talla

Tutocin kasashe 76 masu faretin suka baje a wannan gagarumin fareti da aka yi a birnin Paris da ke nuna shekaru 100 da aukuwar yakin duniya na farko.

Bukin na bana ya sha bamban da na shekarun baya saboda yadda aka kawata bukin da kuma kasashen duniya da suka hallara inda Faransa ta nuna irin dakarun da Allah ya hore mata.

Bukin na zuwa ne bayan da Faransa ta bayyana kawo karshen ayyukan da Sojanta ke yi a kasar Mali, inda suka kori ‘yan tawaye da suka mamaye arewacin kasar.

Faretin na yau, sojoji 3,700 suka yi rawar soja, da shawagi da jiragen sama 50, da nuna wasu abubuwan hawa na soja guda 280, ga kuma dawaki na soja 240.

Jiragen yaki sun yi ta shawagi sararin samaniya, domin burge dubban ‘yan kallo, a wannan rana ta 14 ga watan bakwai da ake bukin samun ‘yancin kan.

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.