Isa ga babban shafi
Canada

Taron Majalisar Dokokin kasashe renon Faransa a Ottawa

An buda taron Majalisar Dokokin kasashe renon Faransa da kuma masu mu’amala da harshen faransanci karo na 40 a birnin Ottawa na kasar Canada, a daidai lokacin da wa’adin aikin babban sakataren kungiyar ta OIF wato tsohon shugaban Senegal Abdou Diouf ke shirin kawo karshe.

Francophonie, kungiyar kasashe renon Faransa.
Francophonie, kungiyar kasashe renon Faransa.
Talla

Yanzu haka dai akwai mutane daga kasashe da dama da suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar neman mukamin sakataren kungiyar, cikinsu kuwa har da Michaëlle Jean ‘yar asalin kasar ta Canada wadda ta tabbatar da hakan a lokacin wannan taro.

Batun kyautata rayuwar mata, duba matsalolin matasa da kuma hanyoyin samar da ci gaba, na daga cikin muhimman batutuwan da taron ya fi mayar da hankali a kai.

Akwai dai manyan baki a wurin wannan taro, da suka hada da shugabannin Majalisun Dokokin kasashe mambobi a kungiyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.