Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta kafa Rundunar Yaki ta musamman a yankin Sahel

Kasar Faransa ta sanar da kafa wata sabuwar Ruduna ta musaman, da za ta yi yaki da ta’adanci a kasashen yankin Sahel. Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian ne ya bayar da sanarwar kafa Rundunar, inda yace Rundunar mai suna Barkhan za ta maye gurbin rudunar Serval wadda ke yaki da ‘yan tawaye a arewacin kasar Mali

thelondoneveningpost.com
Talla

Yace Shugaban kasa Francios Hallande ya umurce mu da mu sake duba yadda Dakarun Faransa ke gudanar da ayyukan su a yankunan Sahel musaman kasar Mali.

Kuma hakan ya kai mu ga daukar kwakkwaran matakai ba wai a kasar Mali kadai ba, harma da wasu yankuna daban.
Ya ce mahimanci wadanan matakai shi ne na kiyaye kasashen yankin Sahel, ko kuma mayar da hankali dama tabatar da tsaro ga hanyoyin da ‘yan Bidinga ko ‘yan ta’ada ke amfani da su wajen shigowa da makamai.

Sanin kowa ne, kasar Libya a yau na daga cikin kasashen da ake shigowa da makamai, kuma za mu gudanar da wadanan ayyukan ne tareda hadin kan kasashe Biyar na yankin Sahel.

Sama da soji 3000 ne zamu aikawa zuwa yankin, kuma daga garin Gao, zuwa Njamena, har birnin Yamey da ke a Jamhuriyar Nijar zuwa Ouagadugoun kasar Burkina Faso za mu iya cewa an kawo karshen ta’adanci na daga cikin muhiman batutuwa da ake kan tautaunawa a kai.

Kudanci Aljeriya, zuwa Arewacin kasar dai na daga cikin wuraren ko hanyoyin da yan ta’ada masu tayar da hankali, ke amfani da su.

Kada mu manta da yankin Libya zuwa Tekun pacific yankin da ke barrazana a wurinmu.

Ba wai muna yin katsalandan ba ne ga matakin tsaro kasashen Afrika, wani matakin ne na kare su dama kara kare kanmu da iyakokin kasashenmu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.