Isa ga babban shafi
Turkiya

Dan Jaridar Jamus ya fice Turkiya

Wani dan jaridar kasar Jamus ya fice daga kasar Turkiya, bayan da aka yi barazana ga rayuwarsa, kan wani labari da ya rubuta game da hadarin da ya yi sanadiyar mutuwar ma’aikata masu hakar ma’adinai sama da 300 a kasar. A cewar dan jaridar wanda ake kira Hasnai Kazim, tun a ranar litinin din da ta gabata ake ta aika ma sa da sakon barazana ga rayuwarsa, tun bayan da ya rubuta wani rahoto da wani mai hakar ma’adinai ya furta kalaman batanci akan Firaministan Recep Tayyip Erdogan.

Masu zanga-zanga suna arangama da 'Yan sanda a kasar Turkiya
Masu zanga-zanga suna arangama da 'Yan sanda a kasar Turkiya Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.