Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya : Hukumar Zabe ta yi watsi da koken ‘Yan adawa

Hukumar Koli ta kula da korafe korafen zabe a kasar Turkiya ta yi watsi da bukatar jam’iyyar hamayya da ke neman a soke zaben Magadan Gari mai cike da rudani da aka yi a Ankara babban birnin kasar.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Istanbul a kasar Turkiya
Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Istanbul a kasar Turkiya Reuters
Talla

Hukumar ta yi watsi da koken ne da Jam’iyyar Republican Peoples Party da ke zargin Jam’iyyar AKP mai mulki ta tabka magudi a zaben.

Amma dan Takarar Jam’iyyar Mansur Yavas yace za su dauki duk matakin da ya wajaba domin kalubalantar Hukumar zaben da kuma jam’iyyar da suke zargi a gaban Kuliya.

Yace duk da Kuri’a daya sai sun tantance yadda aka yi ta je bangaren jam’iyya mai mulki ba.

Jam’iyyar AKP ce ta samu nasara a dukkanin fadin kasar a zaben na Watan jiya inda ta samu gagarumar nasara a Ankara da Istanbul da kuma ake gani tambar zaben jin ra’ayoyin jama’a akan shugabancin shekaru 11 da Firaiminista Recep Tayyip Erdogan ya yi a mulki.

Gwamnatin Erdogan ta fuskanci suka kafafen yada labarai musamman a Intanet game da zaben da kuma batun taimakawa ga rura wutar rikicin kasar Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.