Turkiya
Ma’aikatan kwadago sun shiga yajin aiki a Turkiya
Babbar kungiyar Kwadago a kasar Turkiya ta kira yajin aikin kwana guda sakamakon mutuwar ma’aikatan hako Ma’adinai kusan 300 da suka mutu a cikin kasa. Kungiyar ta kira shiga yajin aikin ne domin juyayin mutuwar ma’aikatan da kuma kira ga gwamnatin kasar ta inganta aikin hako ma’adinai.
Wallafawa ranar:
Talla
A yau Alhamis ne aka fara zaman makoki a kasar Turkiya sakamakon mummunan al’amarin da ya faru da ma’aikatan a garin Soma.
Akwai kuma yanzu daruruwan ma’aikatan da suka makale a cikin kasa, yayin da ake ci gaba da aikin ceto su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu