Isa ga babban shafi
Turkiya

Zaman makoki bayan mutuwar daruruwan mutane a Turkiyya

Firaministan Turkiyya Racep Tayyep Erdogon ya tabbatar da mutuwar mutane 232 a hatsarin da ya faru a wata mahakar ma’adinai da ke kusa da birnin Soma na lardin Manisa a kasar Turkiyya.

Aikin ceto bayan faruwar hadari a mahakar ma'adinan Turkiyya
Aikin ceto bayan faruwar hadari a mahakar ma'adinan Turkiyya REUTERS/ Osman Orsal
Talla

Erdogon, wanda ya kai ziyarar gani da ido bayan faruwa hadarin, ya ce yanzu haka akwai wasu daruruwan ma’aikata da ake zaton cewa suna ci gaba da kasancewa a karkashin kasa bayan ruftawar ma’adinin da suke aiki a ciki.

Rahotanni sun ce mafi yawa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a wannan hatsari sun mutu ne saboda shakar gurbatacciyar iska mai guba a cikin rami, yayin da rahotanni ke cewa sai da jami’an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarzatsa mutanen da ke zanga-zanga a birnin Ankara domin nuna bacin ransu dangane da wannan hatsari.

Tuni dai gwamnatin kasar ta ware kwanaki uku domin zaman makoki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.