Isa ga babban shafi
Turkiya

‘Yan gudun Hijira 18 suka mutu a hatsarin Kwale-kwalen kasar Turkiyya

Akalla mutane 18 da ake zaton cewar ‘yan gudun Hijira ne, suka mutu, bayan da Jirgin Kwale-kwalen da suke ciki ya kife a cikin Ruwa.

Masu aikin ceto
Masu aikin ceto 照片来源REUTERS/Italian Coast Guard/Handout via Reuters
Talla

Wannan hatsarin dai ya auku ne a yankin Ruwan Tsibirin Caicos na yankin Karebiyan.

Hatsarin kuma ya auku ne da sanyin Safiyar Ranar kirsimeti, bayan da ‘yan sanda suka keace Jirgin da ke makare da mutane, koda yake an bayyana ceto akalla mutane 32 daga cikin Fasinjojin Jirgin.

Yanzu haka dai ana can ana lalaben sauran Gawawwakin wadanda suka mutu, a yayin da wani Jirgin saman kasar Amurka ke ta sintiri domin taimakawa masu aikin ceton gano inda sauran mutanen suke.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.