Isa ga babban shafi

Sojin India sun tseratar da masuntan Pakistan daga 'yan fashin tekun Somalia

Sojan ruwan India sun yi nasarar tseratar da ‘yan Pakistan 19 daga ‘yan fashin tekun Somalia wadanda suka kwashe jirgin kamun kifinsu a gab da kasar ta yankin gabashin Afrika.

Matsalar fashin teku na ci gaba da tsananta tun bayan faro hare-haren Houthi a Red Sea.
Matsalar fashin teku na ci gaba da tsananta tun bayan faro hare-haren Houthi a Red Sea. © MICA Center
Talla

‘Yan fashin tekun sun yi garkuwa da masuntan na Pakistan 12 ne tare da kwace jirginsu na kamun kifi mai dauke da tutar Iran da ake kira Al Naeemi lokacin da suke tsaka da aikinsu a teku gab da Somalia.

Sai dai wani rangadin Sojojin ruwa na India karkashin dakarun Sumitra ya kai ga nasarar ceto mutanen su 19 ‘yan kasar Pakistan.

Sumamen Sojin na India cikin tekun da ke matsayin na 2 cikin sa’o’i 36 na zuwa ne bayan sun yi nasarar kubutar da wasu mutane 17 na daban duk dai daga hannun masu fashin tekun a Gulf of Aden.

Hare-haren teku daga ‘yan fashin na Somalia na ci gaba da tsananta tun bayan kaddamar da hare-haren Houthi a Red Sea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.