Isa ga babban shafi
IBM-TEKU

An samu raguwar fashin teku a Duniya karon farko cikin shekaru 27- IBM

Hukumar kula da tsaron gabar teku ta kasa da kasa IMB ta sanar da samun raguwar fashin teku cikin shekarar 2021 karon farko a shekaru 27 musamman tsakanin kasashen yammacin Afrika da a baya aka fi samun wannan matsala.

Fashin teku na taka muhimmiyar rawa wajen kassara hada-hadar kasuwanci tsakanin nahiyoyi.
Fashin teku na taka muhimmiyar rawa wajen kassara hada-hadar kasuwanci tsakanin nahiyoyi. REUTERS
Talla

Cikin rahoton shekara-shekara da hukumar IMB kan fitar ya nuna yadda aka samu fashin teku sau 132 a sassan Duniya, alkaluman da ke matsayin mafi karanci tun bayan shekarar 1994.

Rahoton hukumar na yau alhamis ya ce a kasashen yammacin Afrika sun gamu da fashin teku sau 34 a gabar tekun Guinea cikin shekarar 2021 wanda ya yi kasa da wanda suka gani a 2020 da ya kai 81.

A tsakar gabar tekun na Guinea yankin da ya taso daga kudancin Angola zuwa arewacin Senegal mai tazarar dubunnan kilomita shi ke matsayin yankin mafi hadari a cikin ruwa la’akari da yadda aka fi samun fashi a wajen fiye da kowanne ruwa a tekunan Duniya.

Daraktan hukumar ta IMB Michael Howlett ya yaba da namijin kokarin da ya ce hukumomin tsaron gabar tekun kasashe na yi wanda ya taimakwa wajen raguwar fashin.

Sai dai ya ce nasarar dakile yawaitar fashin tekun kalubale ne ga kasashe wajen ganin sun kara daura damarar yaki da matsalar don tabbatar da tsaron ruwa da nufin baiwa ma’aikatan jirage da harkokin kasuwanci cikakkiyar kariya.

Duk da nasarar raguwar fashin tekun alkaluma hukumar sun nuna yadda aka yi garkuwa da ma’aikatan jiragen ruwa har mutum 57 a cikin shekarar ta 2021 a gabar tekun Guinea mafi girma a nahiyar Afrika.

Hukumar ta ce a 'yan shekarun baya-bayan nan Gabar tekun ta Guinea ta shiga gaban takwararta ta Aden da a baya aka fi samu wannan matsala dukkaninsu a nahiyar Afrika.

Alkaluman da ke kunshe a rahoton, ya nuna yadda can a Singapore aka samu karuwar wannan matsala ta hare-hare da fashin teku da akalla kasha 50 idan aka kwatanta da wanda aka samu a 2020 bayan samun fashin teku har sau 35 mafi yawa tun shekarar 1992.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.