Isa ga babban shafi

Sarkin Charles na III zai dawo aiki a makon gobe bayan hutun jinya da ya tafi

Fadar Buckingham  ta fitar da sanarwar cewa, sarki Charles III zai dawo aiki a mako mai zuwa bayan jinyar cutar daji da ya yi fama da ita.

Sarki Charles na uku kenan, yayin da yake mika gaisuwa ga mutanen da suka ziyarci cocin Magdalene da ke gabashin Ingila, ranar 25 ga Disamba, 2023.
Sarki Charles na uku kenan, yayin da yake mika gaisuwa ga mutanen da suka ziyarci cocin Magdalene da ke gabashin Ingila, ranar 25 ga Disamba, 2023. AFP - ADRIAN DENNIS
Talla

Charles ya tafi hutun jinya kusan watanni uku da suka gabata don mayar da hankali kan kulawar likitci game da cutar dajin da ba a bayyana irin ta ba.

Fadar ta ce Charles zai kai ziyara zuwa cibiyar kula da cutar daji a ranar Talata, ta farko a cikin ziyarce-ziyarcen da zai gudanar a mako mai zuwa.

Daya daga cikin manyan ayyukansa na farko shine karbar bakuncin sarkin Japan da mai dakinsa a watan Yuni.

Fadar ba ta ba da cikakken bayani game da halin da lafiyar sarkin ke ciki ba a halin yanzu, amma dai ta ce tawagar likitocin da ke bashi kulaawa sun ce suna da kwarin gwiwar yana murmurewa akan lokaci sosai.

Ana sa ran sarki Charles zai gana da firaministan Birtaniya Rishi Sunak domin tattaunawa kan batutuwa da dama da suka shafi harkokin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.