Isa ga babban shafi

Matar tsohon Firaministan Pakistan ta yi zargin an zuba mata guba a gidan yari

Matar tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan Bushra Bibi, ta bukaci babbar kotun Islamabad ta bada damar a duba lafiyarta a asibitin Shaukat khanum.

Imran Khan da Matarsa Bushra Bibi
Imran Khan da Matarsa Bushra Bibi © France 24
Talla

Shoaib Shaheen ne ya mika bukatar a madadinta inda ya yi zangin cewa an sanya mata guba a gidan Yarin Banigala don haka ya kamata a gudanar da gwajin lafiyarta a asibitin Shaukat domin tabbatarwa.

A baya-bayan nan wasu rahotanni sun nuna cewa an sanya mata guba a abinci, dalilin da ya sanya a ranar 6 ga watan Afrilu jam’iyyar Pakistan Tehreek Insaf, ta bukaci a duba lafiyarta.

Bukatar hakan ta taso ne bayan wani rahoton likita da cibiyar kimiya ta Pakistan ta fitar, wanda ya gano ba bu wani abu mai dauke da guba da aka baiwa Bushra Bibi a gidan Yarin.

A cewar rahoton cibiyar ciwon ciki ne kurum take fama da shi, to sai dai jam’iyyar PTI bata yarda da rahoton likitocin ba, inda ta kafe akan cewa sakamakon asibitin Shaukat Khanum kadai zata yarda da shi.

Tun a farkon shekarar da muke ciki ne aka yanke wa Bushra Bibi hukuncin daurin shekaru 10 a gidan Yari, sakamakon samunta da laifukan cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.