Isa ga babban shafi

Indiya ta nemi 'yan kasarta da ke aikin soji a Rasha su koma gida

Indiya ta nemi Rasha da ta gaggauta sakin wasu ‘yan kasarta da ke taya sojojin Rashan aiki a makwabciyar kasar, tare da yin kira ga 'yan kasar da su nisanci yakin da ke wanzuwa a Ukraine da aka kwashe tsawon shekaru biyu ana gwabzawa.

Fira ministan Indiya, Narendra Modi kenan tare da shugaban Rasha Vladmir Putin, yayin ganawarsu ta musamman a birnin New Delhi, a watan Oktoban 2018.
Fira ministan Indiya, Narendra Modi kenan tare da shugaban Rasha Vladmir Putin, yayin ganawarsu ta musamman a birnin New Delhi, a watan Oktoban 2018. AP - Manish Swarup
Talla

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Indiya ta fitar ta zo ne bayan da jaridar Hindu ta bayar da rahoton cewa an dauki 'yan Indiya kusan 100 aiki a cikin shekarar da ta gabata karkashin wata kwangila ta tsawon shekara guda.

'Yan kasashe da dama sun nemi aiki tare da sojojin Rasha, ciki har da makwabciyar kasar Indiya Nepal.

Ofishin jakadancin Rasha da ke New Delhi bai ce uffan game da bukatar kasar ta Indiya ba, ko da yake kasashen biyu suna da alaka ta kut da kut, musamman a bagaren kasuwanci da kuma tsaro.

A watan da ya gabata ne Nepal ta dakatar da ba wa 'yan kasarta izinin yin aiki a Rasha da Ukraine bayan da aka sanar da cewa an kashe sojojin Nepal akalla 10 a lokacin da suke fagen daga na taimakon Rasha.

A watan Fabrairun 2022 ne Rasha ta mamaye makwabciyarta Ukraine a wani abin da ta kira farmakin soji na musamman.

Dubun dubatar sojoji daga bangarorin biyu ne suka mutu a yakin da ake ganin mafi muni a Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.