Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci tsaurara matakai don dakile fashin teku a mashigin ruwan Guinea

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci daukar Kwararan matakai domin dakile ayyukan ‘yan fashin teku mashigin ruwan Guinea, wanda ya zama mafi hadari a duniya saboda garkuwa da mutane.

Sojojin ruwan Najeriya yayin sintiri a mashigar ruwan tekun Guinea.
Sojojin ruwan Najeriya yayin sintiri a mashigar ruwan tekun Guinea. © AP Photo/Sunday Alamba
Talla

Kudirin da kasashen Ghana da Norway suka gabatar ya samu amincewar daukacin mambobin kwamitin na Sulhu duk da takun saka da ke tsakanin Rasha da kasashen yammacin duniya wajen yin tir da ayyukan ‘yan fashin jiragen ruwa da ke kara ta’azzara a tekun yammacin Afirka.

Kwamitin ya bukaci kasashe mambobinsa da ke yankin mashigin tekun na Guinea da su dauki matakin gaggawa, na kasa da kuma na shiyya don magance wannan matsala, tare da bayar da tabbacin samun taimakon kasashen duniya, a duk lokacin da wata kasa ta nemi bukatar dauki.

Kwamitin ya kuma yi kira ga daukacin kasashen yankin da su samar da nasu tsare-tsare tare da samar da tsauraran dokokin hukunta ‘yan fashin teku a kasashensu.

A cewar wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, cikin mutane 28 da aka yi garkuwa da su a jiragen ruwan duniya a shekarar 2020, 27 daga cikinsu a mashigin tekun Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.