An soma taron kolin kasashen musulmi na OIC karo na 15 a birnin Banjul
Shugabanni da dama daga kasashen musulmi sun fara isa birnin Banjul na kasar Gambia inda ake soma taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC karo na 15,taron da zai tattauna batutuwa da dama har da rikicin Hamas da Isra’ila.
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga Banjul na bayyana cewa,kusan kasashe 57 ne suka aika da wakili a taron da za a soma ranar Lahadi sai dai ,tsirarun shugabannin kasashen Afirka ne suka yi wannan balaguron, kamar na Senegal.
Babban sakataren kungiyar Hissein Brahim Taha a yayin bude taron ya na mai cewa "wannan taro na Banjul ya zo ne a cikin yanayi mai tsanani da ba a taba ganin irinsa ba a cikin al'ummar Falasdinu, Isra’ila na ci gaba da kisan fararren hula a idanun manyan kasashen Duniya.
Hissein Brahim Taha ya yi kira ga kasashen kungiyar OIC da su “kara kaimi da hadin kai wajen tabbatar da al’ummar Falasdinu”, tare da bayyana cewa dole ne a dauki matakin musamman kan Falasdinu a karshen taron a ranar Lahadi.
A watan Nuwamban shekarar 2023, kungiyar ta gana a birnin Riyadh don gudanar da wani taron hadin gwiwa da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, inda ta yi Allah wadai da matakin da sojojin Isra'ila suka dauka a Gaza, amma ta kaurace wa sanar da daukar matakan ladabtarwa na tattalin arziki da siyasa kan Isra'ila.
Wannan taron dai ya nuna rarrabuwar kawuna a yankin dangane da yadda za a mayar da martani ga rikicin, dangane da fargabar barkewar rikici a yankin.
A ranar Asabar ne dai hankali ya fi karkata kan kasar Masar, inda wata tawaga daga Gaza ta isa don tattaunawa kan shirin tsagaita wuta a Gaza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu