Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Mali ta bude taron duba lamuran da zasu amfani kasar

Gwamnatin mulkin sojin Mali ta shirya wani babban taron tattauna batutuwan da suka shafi kasar ta yadda za’a samar da mafita mai dorewa.

La localisation de Mondoro, au Mali.
La localisation de Mondoro, au Mali. © Studio FMM
Talla

Taron dai za’a fara shine nan da kwanaki 6 masu zuwa wadda zai kunshi duk wani mai ruwa da tsaki kan lamuran ci gaban kasar.

Gwamnatin mulkin sojin ta  Mali ta shriya ganawarce sakamakon irin matsin lambar da ta ke fuskanta ne akan ganin ta mai da mulkin ga hannun farar hula, baya ga tabarbarewar tsaro da kuma koma bayan tattalin arziki da kasar ke fama dasu.

Kasar ta yammacin Afirka ta fuskanci juyin mulki ne akai-akai a shekarun 2020 zuwa 2021, wadda tun a wancan lokacin sojin ke alkawarin mika mulkin ga hanun farar hula sanadiyar matsin lambar da kungiyar ECOWAS ta yi mata a watan fabrairu.

Sai dai sojojin sunyi kunnen uwar shegu kan kiraye-kirayen da suke samu daga ciki da wajen kasar, yayin da suke danganta jinkirin da ake fuskanta da matsalolin hare-hare na masu ikrarin jihadi a kasar, wanda ya haddasa rashin kwanciyar hankalin da har za a iya gudanar da zabe a kasar.

Hakanan, baya ga adawa ta abokan hamayya da bibiya irin ta ‘yanjarida da ta kungiyoyin fararen hula sai mahukuntan kasar ta Mali suka dakatar da dukkanin harkokin jam’iyun siyasa tare da rushe kungiyoyin fararen hular kasar da ke rajin a mayar da mulki ga turbar dimokaradiya a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.