Isa ga babban shafi

HRW ta zargi masu ikirarin jihadi da mayakan sakai da laifin kisan kiyashi a Mali

ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta JNIM da mayakan sakai na mafarauta da kisan fararen hula 45 a tsaƙiyar Mali.

ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta JNIM da mayakan sakai na mafarauta da kisan fararen hula.
ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta JNIM da mayakan sakai na mafarauta da kisan fararen hula. REUTERS - PAUL LORGERIE
Talla

Cikin wani rohoto da ta fitar ranar Laraba kan aika-aikar, Human Right Watch ta ce masu iƙirarin jihadi da ke da alaka da al-Qaeda sun aikata kisan kiyashi.

Mafarauta

Ƙungiyar ta kare hakkin bil adama ta kuma yi karin bayani game da cin zarafi daga ƙungiyar mafarauta ta Dozo, wadanda tsawon shekaru suka rikide zuwa masu kare al'ummarsu daga hare-haren masu ikirarin jihadi.

Rahoton ya ce dukkan bangarorin biyu, sun aikata aika-aikar cikin watan Janairu a tsakiyar kasar Mali.

A ranar 27 ga watan Janairu, da misalin karfe 6 na yamma, masu iƙirarin jihadi da dama kan babura da motoci dauke muggan makamai sun kai hari kauyukan Ogota da Ouembé, na yankin Mopti

Hanyoyin da aka bi wajen tantance zargin

A cewar bayanan da kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta tantance daga shedun kai tsaye 25, da masu fafutuka na kasar Mali da kuma mambobin kungiyoyin kasa da kasa, da taimakon hotunan tauraron dan adam, masu ikirarin jihadi sun kashe mutane 32 a wannan a ranar , wadanda suka hada da mata da tsofaffi da yara tare da kone gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.