Isa ga babban shafi

Matsalar fashin teku ta ragu zuwa mafi karancin adadi cikin shekaru 14

Hukumar tabbatar da tsaro a teku ta kasa da kasa mai hedikwata a Faransa, ta ce matsalar fashi akan ruwa ta ragu zuwa mafi karancin adadi cikin shekaru 14, a 2022 da ta gabata.

Wani jirgi  yayin barin tashar jiragen ruwa ta Vladivostok da ke kasar Rasha.
Wani jirgi yayin barin tashar jiragen ruwa ta Vladivostok da ke kasar Rasha. AP
Talla

Rabon da a samu wannan sauki na ta’addancin ‘yan fashin teku, tun a shekarar 2008, kamar yadda hukumar samar da tsaron a tekun ta MICA ta bayyyana

Hukumar wadda jami’an sojin ruwa na Faransa da hadin gwiwar takwarorinsu na wasu kasashe ke gudanarwa, ta ce sau 300 ta samu rahoton ayyukan fashin teku a shekarar bara.

MICA ta ce, a mashigin ruwan Guinea da ke yammacin gabar tekun Afirka da ake ganin shi ke kan gaba wajen fama da matsalar fashi da makami, jirage uku kawai akai kai wa hari a shekarar 2022, amma a 2019 jirage 26 ‘yan fashi suka afka wa.

Rahoton ya kara da cewar, a yankin mashigin ruwan na Guinea, adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ya ragu matuka zuwa biyu a shekarar 2022, daga mutane 146 a shekarar 2019.

Sai dai jami’ai sun yi gargadin cewa ya kamata a cigaba da taka-tsantsan domin kuwa ana iya sake komawa gidan jiya.

Bincike dai ya nuna cewar, akasarin tsaffin ‘yan fashin teku sun koma wasu ayyukan da suka hada da tace mai ba bisa ka’ida ba, ko kuma safarar danyen man da aka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.