Najeriya: 'Yan sanda sun ceto masunta 28 a hannun 'yan fashin teku a Akwa Ibom
‘Yan sanda a jihar Akwa Ibom da ke kudu maso kudancin Najeriya sun ceto wasu masunta 28 daga hannun ‘yan fashin teku da suka yi garkuwa da su bayan sun sace su a yayin da suke bakin aiki.
Wallafawa ranar:
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Olatoye Durosimi ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da jawabi ga manema labarai a jiya Juma’a.
Ya ce yana samun wannan labarin yin ya yi maza ya umurci dakarunsa da ke aikin sintiri a ruwa da su ceto so, kuma ba su bata lokaci ba wajen kwato mutanen a hannun masu garkuwa.
Kwamishinan ya ce wadannan ‘yan fashin teku suna sajewa ne da masu kamun kifi suna aikata laifuka a teku, yana mai cewa yanzu haka sun damke 5 daga cikinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu