Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiyya ta bukaci Malam Gulen ya daina kula harkokin Siyasa

Firaiministan Turkiya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi kira ga fitaccen Malamin addinin Islama nan na kasar, wato Fethullah Gulen da ya daina tsunduma bakin shi a harkokin siyasar kasar. A baya dai Gulen ya kasance wani na hanun daman Firaiminista Recef Tayyeb Erdogan kamin ala’murra su yi tsami a tsakaninsu

Babban Malamin addinin musulunci Fathullah Gulen
Babban Malamin addinin musulunci Fathullah Gulen en.wikipedia.org
Talla

Firaiministan Erdogan dai ya jima yana zargin Fathullah da cewa shi da magoya bayansa ne suka kaddamar da binciken cin hanci da rashawa a kasar, lamarin da ya girgiza gwamnatin Erdogan, bayan samun wasu daga ministocinsa da hanu dumu-dumu a binciken.

A wani gangami da Erdogan ya shirya a Kudu maso yammacin kasar a garin Isparta a ran lahadi, Firaiministan ya ce yana kalubalantar Malamin, da ya koma kasar ta Turkiya idan yana da gaskiya.

Shi dai Gulen da magoya bayansa, su suka marawa jamiyar AKP ta Erdogan baya a zaben shekarar 2002, wato tun kamin abokantakarsu ta yi tsami da Firaiministan.

Wannan takaddama da ke faruwa tsakanin shugabannin biyu dai, na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar ta Turkiya ke fuskantar wani muhimmin zabe a ranar 30 ga watan nan na Maris.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.