Isa ga babban shafi
EU-Pakistan

Malala Yousafzai ta karbi kyautar Sakharov ta Turai

Dalibar kasar Pakistan Malala Yousafzai da Mayakan Taliban suka harba ta karbi kyautar karramawa ta Sakharov daga Kungiyar Tarayyar Turai saboda fatawar da dalibar ta ke yadawa na inganta ‘yancin karatun yara kanana.

Malala Yousafzai da Taliban suka harba a Pakistan ta rike kyautar Sakharov ta Turai tare da Shugaban Majalisa Martin Schulz
Malala Yousafzai da Taliban suka harba a Pakistan ta rike kyautar Sakharov ta Turai tare da Shugaban Majalisa Martin Schulz REUTERS/Vincent Kessler
Talla

A lokacin da zai mika wa Malala Kyautar jagoran Majalisar Turai Martin Schulz ya jinjina wa Dalibar mai shekaru 16 na haihuwa, yana mai cewa Jaruma ce da ke kokarin samar da rayuwa ga Miliyoyan yaran da ba su da gata.

Malala ita ce ta 25 da ta karbi Kyautar Sakharov da mafi yawanci ake ba masu fafatukar kare hakkin Bil’adama a duniya.

Nelson Mandela Tsohon Shugaban Afrika ta kudu da tsohon Sakatare Janar na Majaisar Dinkin Duniya suna cikin wadanda suka taba karbar kyautar.

Malala ta sadaukar da kyautar ne ga ‘Yayan talakawan Pakistan da kuma kungiyoyin kare hakkin Bil’adama a duniya.

Duk shekara ne ake gabatar da Kyautar Sakharov a zauren Majalisar Turai domin tuna Andrei Sakharov Masani ilimin Pysics a Tsohuwar daular Soviet.

A jawabin Malala tace yara yanzu ba su bukatar iPhone ko Chocolates illa Biro da Takarda.

Malala Ita ce dalibar da Mayakan Taliban suka harba bayan ta furta kalaman adawa da su. A shekarar 2009 ne aka kwashe ta zuwa Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.