Isa ga babban shafi
Pakistan-Afghanistan

Taliban ta aika wa Malala da wasikar Martani

Wani Babban jami’in kungiyar Taliban a kasar Pakistan, Adnan Rasheed, ya rubuta wasika zuwa ga Malala Yusoufzai, matashiyar da ‘Yan kungiyar suka harba,  yana mai  zargin Dalibar ta bata wa kungiyar suna tare da bin dabi'un Turawa. 

Malala Yousafzai da Taliban suka harba tana karatu a Fadar Sarauniya  Elizabeth a Birmingham,
Malala Yousafzai da Taliban suka harba tana karatu a Fadar Sarauniya Elizabeth a Birmingham, Reuters/Hospital Queen Elizabeth
Talla

Rasheed wanda tsohon jami’in sojin sama ne, ya bayyana nadamarsa na harin da aka kai wa Malala, sai dai ya ce harin ba shi da nasaba da neman ilimi, sai dai don batawa kungiyar suna wajen rubuce rubucen da ta ke yi.

“Abin mamaki ne kina ikrarin cewa an harbe ki ne saboda batun neman ilimi, wannan ba shi ne dalilin ba illa saboda sunan da kike ba ta mana.” Inji Rasheed.

Masana suna ganin, Taliban sun aika  wa Malala da wasikan ne domin mayar da martani ga kalaman da ta yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

A Cikin wasikar, Adnan Rasheed ya bukaci Malala ta dawo gida Pakistan.

A watan Oktoba ne kungiyar Taliban suka harbi Malala mai shekaru 16 a Pakistan bayan ta kammala wani yakin tabbatar da karun ‘ya’ya mata.

Jawabin dalibar a Majalisar Dinkin Duniya ya ja hankalin duniya, Kuma Malala tace zata ci gaba da gwargwarmaya domin ci gaban ilimi a duniya.

Rasheed ya zargi Malala tana kokarin yayata tsarin ilimin Turawan mulkin Mallaka wanda ya sabawa karantarwar Addini.

“Ina ba ki shawara ki dawo gida domin ki rike addininki da al’adunki, kina iya shiga makarantar Islamiya kusa da gidanku domin karfafa kalmar Allah” a cewar Rasheed a cikin wasikarsa.

A baya an taba yanke wa Rasheed hukuncin Kisa a 2003 akan zargin kai wani hari a Pakistan zamanin mulkin Musharraf, kafin Rasheed ya tsere daga gidan yari.

Malala tace Malami da Dalibi da Biro da Takarda suna iya canza duniya, a cikin jawabinta a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.