Isa ga babban shafi
MDD-Pakistan

Malala za ta ci gaba da gwagwarmaya

Dalibar kasar Pakistan Malala Yousafzai da Mayakan Taliban suka harba, ta sha alwashin ci gaba da gwagwarmaya a wani jawabi mai jan hankali da ta gabatar a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Malala Yousafzai a Zauren Majalisar Dinkin Duniya tana gabatar da jawabi
Malala Yousafzai a Zauren Majalisar Dinkin Duniya tana gabatar da jawabi REUTERS/Brendan McDermid
Talla

“Sun yi tunanin harsashensu zai iya kawo karshen mu, amma basu yi nasara ba” a cewar Malala a loacin da ta ke gabatar da jawabin muhimmacin ilimi ga rayuwar al’umma.

Dalibar tace harbin Taliban ya cire mata tsoro da fargaba, illa samun karfi wajen ci gaba da gwagwarmaya.

Malala ta yi shigar tufafi ne irin na tsohuwar shugabar Pakistan da aka kashe Benazir Bhutto.

A ranar 12 ga watan Oktoban bara ne Mayakan Taliban suka harbi Malala tana cikin Mota kirar Bus a Pakistan, amma dalibar tace bata bukatar daukar fansa illa tana bukatar samarwa ‘ya’yan mayakan Taliban ilimi da sauran mayaka a duniya.

Malala tace Littafi da Biro sune garguwar ci gaban al’umma.

“Dalibi da Malami da Biro da Littafi kan iya canza duniya” inji Malala.

Ana ganin dai Malala na iya samun kyautar Nobel ta zaman lafiya, amma har yanzu Taliban sun ce tana cikin wadanda suke farauta.

Malala Yousafzai daliba ce da ke gwargwarmayar tabbatar da ilimin ‘yaya mata.

A wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya, an kiyasata cewa kimanin yara kanana Miliyan 57 ne basu zuwa makaranta, rabinsu kuma daga Syria saboda yakin da ake ci gaba da gwabzawa a kasar.

A wani Rahoton Ban Ki-moon na karatun yara kanana a kasashen da ake rikici, an kiyasta kimanin yara 115 ne aka kai wa hari a kasar Mali, 321 kuma a yankunan Falesdinawa, a kasar Afghanistan 167 sai a kasar Yemen 165.

Kasar Pakistan ce ke da yawan yara Miliyan 5 da ba su zuwa makaranta, sai Najeriya mai yawan yara Miliyan 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.