Isa ga babban shafi
Pakistan-Syria

Malala ta nemi a ilmantar da ‘Yan gudun hijira a Syria

Matashiya mai fafutukar ganin an bai wa ‘ya’ya mata ilimi a kasar Pakistan, Malala Yousufzai, ta bukaci shugabannin kasashen duniya su bayar da gudumawar kudi Dala Miliyan 175 don ilmantar da dimbin yara ‘Yan gudun hijirar da suka kwararo zuwa kasashen da ke makwabtaka da kasar Syria.

Malala Yousafzai, Sanye da Tufafin Tsohuwar Firaministan Pakistan Benazir Bhutto, a lokacin da ta ke gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya bayan ta murmuje daga harin bindiga na Kungiyar Al Qaeda
Malala Yousafzai, Sanye da Tufafin Tsohuwar Firaministan Pakistan Benazir Bhutto, a lokacin da ta ke gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya bayan ta murmuje daga harin bindiga na Kungiyar Al Qaeda REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Malala tace tana jin zafin abinda ya ke faruwa a kasar Syria, domin sun taba fuskanci irin matsalar a kasar Pakistan.

Hukumar kula da ilimin yara ta Majalisar Dinkin Duniya tace yaran Syria 257,000 ke neman ilimi a Lebanon, inda tace adadin na iya akaruwa zuwa 400,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.